Wani mutum Mai kishin Tallafawa matasa da mata Marayu Da gajiyayyu Mai suna Alh Ibrahim Linda Mai shine ya bayyana cewa baya Kyashin fitar da hakkin Allah a cikin Dukiyar Da ya bashi tun daga Naira Miliyan Daya zuwa sama.

Alh Ibrahim ya bayyana hakan ne a safiyar yau Lahadi a lokacin da yake Mika Kudaden tallafi ga Mata da matasa dalibai har ma da masu kananan sana’oi.
Inda yace babban abin da zai taimaka wajen kare Dukiyoyi shine tafiyar dashi kamar yadda Allah yayi umarni.
Haka zalika yayi Kira da masu hannu da shuni da su rika tallafawa mabukata haka ne kawai zai tsare Dukiyoyi daga fadawa masifu.

Ya kuma yi Kira da wayanda suka samu tallafin dasuyi amfani da abin da suka samu ta hanyar Da ya dace ba wai su banzatar da Shi.

Cikin Wayanda suka Amfana da tallafin harda Wayanda Mujallar Matashiya ta koyar dasu sana’oi daban daban.
Akalla Mutane kimanin 100 ne suka karbi tallafin dubu goma goma. A hannun Alh Ibrahim Linda Wanda ya wakilta Asma’u Sadiq wajen tattaro mutanen da ya dace su karbi tallafin.