
Gwamnatin Tarayya ta bayyana “alhini da jimami matuƙa” bisa mummunar fashewar tankar mai da ta auku a Essa da ke Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja kwanaki kaɗan da suka wuce, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Laraba, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce: “Muna taya Gwamnatin Jihar Neja da al’ummar ta jimamin wannan babban rashi.

“Wannan abin takaici ya sake tunasar da mu illolin da haɗarin fashewar tankar mai ke haifarwa ga rayuka da dukiyoyi a cikin al’ummomin mu.”
Alhaji Idris, wanda shi ma ɗan asalin jihar ne, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta yi matuƙar baƙin ciki ganin cewa duk da wayar da kai da gargaɗi da aka sha yi kan haɗarin ɗibar mai daga tankokin da suka faɗi, har yanzu wasu mutane suna ci gaba da irin wannan gangancin da zai iya kai su ga halaka.
Ya ce: “Rayuwar kowane ɗan Nijeriya tana da muhimmanci, kuma irin waɗannan abubuwan da za a iya gujewa suna tuna mana muhimmancin kulawa da bin umarnin tsaro, musamman a lokutan gaggawa.”
Ministan ya ƙara da cewa: “Muna yaba wa yadda Gwamnatin Jihar Neja, jami’an tsaro, da ma’aikatan agajin gaggawa suka gaggauta ɗaukar mataki wajen kashe wutar, da ceto waɗanda suka tsira, da kuma tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa.”
Ya bayyana cewa an umarci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta haɗa gwiwa da gwamnatin Jihar Neja wajen ci gaba da bayar da taimakon gaggawa da jinya ga waɗanda abin ya ritsa da su da iyalan su.
Haka kuma ya ce Gwamnatin Tarayya ta umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a duk faɗin ƙasar nan, musamman a yankunan karkara da wuraren da ake fuskantar irin waɗannan haɗurra, domin hana maimaituwar irin wannan bala’i.
Ministan ya ƙare da cewa: “Tunanin mu da addu’o’in mu suna tare da waɗanda abin ya shafa, da iyalan su, da al’ummar Jihar Neja baki ɗaya a wannan lokaci na jimami. Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma ba iyalan su haƙuri da ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.”