
Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da Naira Biliyan 32.9 don gudanar da shirin Basic Health Care Provision Fund (BHCPF), wanda zai tallafawa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin ƙasa baki ɗaya. Wannan shi ne zagaye na uku na wannan shirin a bana.


Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken Jar Wasiƙa “The Red Letter”, inda ya jaddada cewa kudaden sun riga sun fara shiga asusun ajiyar kuɗi na cibiyoyin kiwon lafiya na gundumomi a duk faɗin ƙasar.
Pate ya ce wannan mataki na nufin bai wa al’ummomi ikon tsara yadda za su kashe kudaden domin tabbatar da cewa kuɗin ya samar da ingantaccen sakamako ga jama’a.
Ya ce gwamnatin tarayya ta cika nata alkawari wajen samar da kudaden, yanzu al’ummomi ne ke da hakkin tabbatar da cewa an yi amfani da su yadda ya dace.
Ministan ya yi kira ga kowane ɗan Najeriya da ya tashi tsaye wajen kare lafiyar jama’a ta hanyar shiga cikin kwamitocin kula da asibitoci, duba yadda ake kashe kudaden, da kuma tabbatar da gaskiya da bayyananniyar hanya wajen amfani da su.
Ya ƙara da cewa gwamnati tana son ganin wannan saƙo ya isa kowace unguwa, gunduma da gida, don tunatar da ‘yan ƙasa cewa inganta lafiyar Najeriya abu ne da yake hannun yan Najeriya.