Jami’ar Abuja ta kori malamanta guda biyu da suka Kai matakin Farfesoshi bisa zargin su day lalata da dalibai mata.
.haka zalika jami’ar ta rage wa wasu Malaman matakin karatun da dai bisa zargin su da Muamala da dalibai.

Cikin wata sanarwa da babban Jami’in yada labaran Jami’ar Dr Habib Yakub ya fitar ya bayyana sunayen Farfesoshin da suka kora Wanda suka hada da: Farfesa Adeniji Adebayo, daga sashin koyar da ayyukan Gona, sai Farfesa Agaptus Buzo-Chibuzo Orji dake sashin koyar da kimiyar Ilimin Muhalli.
Haka kuma Jami’ar ta ragewa Dr Robert Dajal da Mista Gana Emmanuel Sunday Matakin katatu.

