Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya reshen jihar Ogun sun gudanar da zanga zanga ta nuna ƙin amincewa da tuɓe alƙalin-alƙalai na ƙasar Najeriya.
Ɗaliban waɗanda suka nuna ƙin amincewarsu ta hanyar rubutu a allon riƙewa sun nuna damuwarsu kan yadda shugaban ƙasar ke iƙirarin yaƙi da cin hanci da rashawa.
a daidai lokacin ne kuma ƙungiyar lauyoyin Najeriya suka fara zanga-zanga kan matakin dakatar Babban Alkalin Najeriya Walter Onnoghen a gaban hedikwatar kungiyarsu (NBA) a Abuja ranar Litinin.

Masu zanga-zangar sun ce suna so ne Shugaba Muhammadu Buhari ya soke matakin dakatar da babban alkalin kasar.
A ranar Juma’a ne Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen bayan kotun da’ar ma’aikata (CCT) ta umarce shi da ya yi hakan saboda tuhumarsa da kin bayyana kadakorinsa.

Haka kuma shugaban ya rantsar da Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin mukaddashin babban alkalin kasar.

Lauyoyin sun bukaci kungiyar NBA da ta fara yajin aiki kuma hukumar da ke kula da bangaren shari’ar da ta dakatar da sabon mukaddashin Alkalin Alkalin.
Yayin da suke zanga-zanga, an samu wani ayarin masu zanga-zanga da ya isa wurin, inda suke goyon bayan matakin Shugaba Buhari na dakatar da Onnoghen.
a wani cigaban kuma An girke ‘yan sanda a gaban hedikwatar kungiyar NBA da ke Abuja ranar Litinin
A safiyar ranar Litinin, an girke ‘yan sanda a gaban hedikwatar kungiyar NBA, inda mambobin suka yi wani taron don tattauna batun dakatar da Alkalin Alkalin.
Kungiyar lauyoyin ta kira wani taron gaggawa a ranar Litinin, bayan Shugaba Buhari ya dakatar da Mista Onnoghen.
Daya daga cikin lauyoyin da suka shiga zanga-zangar, sun ce Shugaba Buhari bai bi ka’ida ba wajen dakatar da alkalin.
Ya ce gwamnati ta nuna son kai don ya kamata ne kafin shugaban ya dauki matakin sai ya rubuta wa majalisar dattawan kasar.