A kalla kimanin mutane uku ne suka rasa rayukansu dangane da zazzabin cutar Lassa da ake zargi cutar takai mutanen har lahira a asibitin koyarwa na malam Aminu kano.

Cikin wadanda suka rigamu gidan gaskiya harda likitocin asibitin su biyu.

Cikin wata sanarwa data gudana hukumar asibitin AKTH ta sanarda da farabinciken gaggawa kan wasu mutane da ake zargin sunkamo da cutar zazzabin Lassa.

A wayewar garin yau talata 21-01-2020 wasu rahotanni sukace annobar cutar data barke a asibitin, wanda yahada da wasu likitoci biyu dasu duba mara lafiyar da ake zargi azo da cutar sun mutu har lahira, sannan wasu mutane uku da ake kautata zaton sunyi mu’amula da mai cutar suna kwance cikin halin jinya yanzu haka.

A wata sanarwa mai dauke da sahannun mukaddashin shugaban asibitin Dr Auwalu Umar Gaida, tace toni aka dauki jinin da ake zargi sunkamo da cutar zuwa dakin bincike domin tabbatar da ingantattacen bincike akan lamarin.

Sai dai zuwa yaunzu antsara yadda za’agudanar da taron wayar da kan ma’aikatan asibitin game da hanyoyin da zasubi don tsira daga annobar a gobe laraba.

Sanarwar ta kuma bukaci ma’aikatan asibitin dasu kwantar da hankalinsu, tare da yin takatsantsan alokutan dasu duba marasa lafiya sannan su kauce yada bayanai dangane da wannan al’amarin a shafukansu na yanar gizo-gizo dan kaucewa tayarwa al’umma hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: