Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje ya amince da biyan kuɗi naira miliyan 100 ga ɗaliban da ke karatun mastas da PHD a ƙasar faransa.

Ɗaliban da suka kasance masu koyarwa ne a kwaleji daban daban a Kano ciki har da kwalegin kimiyya da fasaha da ke garin wudil da kuma jami ar Yusuf Maitata Sule.

Haɗin gwiwar da aka yi daƙasar Faransa da aka sawa suna Kano/France Join Scholarship Programme kuma ɗaliban da aka tura na karatu a wasu makarantu daban daban a ƙasar.

Mai sanya idanu kan lamarin kuma babban mataimaki ga gwamnan Kano kan ilimi mai zurfi Dakta Dakta Hussaini Aƙilu Jarma ya tabbatar da cewar gwamnatin Kano za ta tabbatar da cewar ɗaliban sun kammala karatunsu lami lafiya ba tare da tsaiko ba.

Ana sa ran ɗaliban za su kammala karatun a watan Agustan shwkarar 2020 da muke ciki .

Leave a Reply

%d bloggers like this: