Labarai
Ba mu hana Adam Zango zuwa Kano kallon fim ba – Afakallah


Shugaban hukumar tace fina finai da ɗab’i a jihar Kano Mallam Isama il Na’abba Afakallahu ya bayyana cewar bhukumar ba ta hana Adam Zango zuwa kano kallom fim ba.

Afakallahu ya ce a sanarwar da jarumin ya yi ya nuna cewar zai yi wani kwarya kwaryar wasa ne kuma hakan ce ta sa yin gargaɗi a kansa saboda rashin cika ƙa idar da hukumar ke da shi.
Cikin zantawarsa da Mujallar Matashiya Afakallahu ya ce babu wani yunƙuri na hanashi zuwa kallom fim sai don bayyana cewar yana son ganawa da masoyansa tare da raba musu kyautuka wanda hakan yayi dai dai da keta dokar hukumar muddin bai nemi sahalewar hakan ba.

A gefe guda kuwa Afakallahu ya musanta zargin da jarumin yayi na cewar hukumar na haɗa kai da wasu mutane a masana antar don dadidhe tauraruwarsa a masana antar wanda ya ce ” An sanka ba sanin shanu ba, kuma kowa ya san yadda kake kuma jama a ne za su yi alƙalanci a kanka” inji Afakallah.

Jarumin dai ya bayyana cewar ya fita daga masana antar gaba ɗaya har ma yayi zargin cewar ko da ya je hukumar don yin rijista to kuwa hakan ba zai yi maganin matsalar da yake fuskanta ba.

Labarai
Tsadar Karatu Na Iya Sa Rabin Ɗaliban Jami’a Su Gudu – ASUU


Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta ce kashi 50% na ɗaliban da ke karatu na iya ajiyewa saboda tsadar karatu da ake ciki a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Frafesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyana haka ya ce nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa ɗaliban da ke karatu a jami’o’in ƙasar kashi 50% daga ciki na iya ajiye karatun nasu.
A wata hira da aka yi da shugaban a gidan talabiji na Channels ranar Lahadi da daddare, ya gargaɗi ɓangaren ilimi na ƙasar da su farga a kan abinda ka iya faruwa.

Sai dai ya alaƙanta ƙara kuɗin da jami’o’i su ka yi da mafi ƙarancin albashin da ake biya na naira 30,000 a ƙasar.

Sannan ya ce akwai hatsari mai yawan gaske idan aka samu ƙarin matasa masu yawa da su ka bar makaranta.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata gwamnatin Najeriya ta ce ta ƙarawa malaman jami’a albashi da kashi 30 ga masu matsayin farfesa.
Labarai
Gobara Ta Kama A Kotun Ƙoli Ta Najeriya A Abuja


Rahotanni daga baban birnin tarayyar Najeriya Abuja na tabbatar da cewar kotun ƙoli ta kama da wuta.

Ofishin alƙalai uku aka ruwaito sun ƙone bayan tashin gobarar.
Godan jaridar Arise ya ruwaito cewar, wutar ta kama wai ɓangare na cikin kotun.

Sai dai ba a san sanadin tashin gobarar ba.

Wannan dai itace gobara da aka yi a kusa-kusa wadda ta shafi ofishin gwamnati.

Ko a watan Mayun shekarar da mu ke ciki, gobara ta kama a rundunar sojin samar Najeriya.
Yayin da a shekarar da ta gabata ta 2023 ma’aikatar kuɗi ta tarayya wani ɓangare ya kama da wuta.
Labarai
Amuruka Ta Gargaɗi Ƴan Ƙasar Mazauna Najeriya Kan Ziyartar Wasu Jihohi Har Da Kano


Ƙasar Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su kiyaye wajen ziyartar wasu jihohi da ka iya faɗawa cikin hatsari.

Sanarwar na zuwa ne bayan gudanar da wani bincike da su ka gano an samu ƙaruwar aikata manyan laifuka a jihohin.
Jihohin sun haɗa da Borno, Adamawa, Yobe, Kogi, Bauchi, Kaduna, Kano, Gombe, Bayelsa, Rivers, Enugu da jihar Bayelsa.

Sauran jihohin su ne Imo, SokOto, Zamfara, Katsina, da jihar Abia.

Ƙasar ta gargaɗi mutanenta da su kiyaye wajen ziyartar waɗannan jihohi domin su na iya faɗawa cikin tarkon masu garkuwa da mutane ko wasu miyagun laifuka.

Binciken da su ka yi sun gano cewar masu satar mutane domin neman kuɗin fansa na amfani da ƙarin mutane a wasu sassa domin cimma muradinsu.
Sannan gwamnatin Amurukan ta buƙaci ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su ƙara sanya idanu a kan dukkanin zirga-zirgarsu don gudun faɗawa hatsari.
-
Mu shaƙata8 months ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Al'ada4 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labaran ƙetare4 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Labarai4 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini3 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida
-
Labarai6 months ago
Akwai Jihohi Goma Da Zaɓen Gwamna Bai Kammala Ba A Najeriya Ko Har Da Kano?
-
Girke girke5 years ago
YADDA AKE LEMON SHINKAFA