Hukumar Dake yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin kasa zagon Kasa EFCC ta Cafke Kwamishinan Ayyuka na musamman na Jihar Kano Mukhtari Ishaq bisa zargin da sama da fadi da wasu kudade da suka kai Miliyan 76.

Kudaden dai sun bata ne a lokacin da yake Matsayin Shugaban karamar hukumar Birne da kewaye.

Mai magana da yawun Hukumar Reshen jihar kano Tony Orilade ya ce ana zargin Kwamishinan ne da juya akalar kudaden bayan an fitar dasu da zimmar gudanar da manyan Ayyukan cigaba na karamar hukumar.

Haka zalika Hukumar na zargin sa da cire naira Dubu 30 cikin Albashin yan Majalisar zartarwar karamar hukumar Birne da kewaye.

Madogara
Kano Focus

Leave a Reply

%d bloggers like this: