Matashin ya yi ƙoƙarin hallata budurwar tasa ne don rufin asirinsa ganin cewa ciki ya bayyana kuma ta ce shi ya mata.

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi mai suna Shafi u Haruna mai shekaru 27 bisa zargin kashe budurwarsa bayan ya mata ciki.

Ana zargin Shafi u da hallaka budurwarsa mai suna Hamsiya Lawan mai shekaru 14 mazauna garin  Bidigau a ƙaramar hukumar ƙanƙara.

Matashin ya ɗauki budurwar tasa zuwa wani daji inda kuma ya ɗauki dutse ya yi ta dukanta da shi a ka har ta rasa ranta.

Lamarin ya faru ne tun a watan disamban shekarar da ta gabata kuma an kamashi ne a ranar Talata uku ga watan Maris ɗin da muke ciki.

Tuni rundunar ta duƙufa don zurfafa bincike a kansa kuma za ta gurfanar da shi a gaban kotu bayan ta kammala bincike.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun ƴan sanda a Katsina Gambo Isah ya fitar, rundunar ta yi holen mutane da dama ciki har da wasu masu garkuwa da mutane da rundunar ta kashe tare da kwato wasu makamai daga hannun ƴan bindiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: