Mutane 6 da aka yi musu gwaji aka samesu suna dauke da Cutar Corona Virus sun tsere daga wurin da aka Killace su.

Lamarin ya faru ne a garin Ejiagbo na Jihar Osun.

Rahotanni dai sun bayyana cewa ana kyautata zaton mutanen sun dawo ne daga Garin Abidjan babban birnin Ivorycoast.

Bayan sun dawo ne aka gwada su aka gano suna dauke da Cutar.

Sai dai Gwamnatin jihar Osun sun bayyana cewa mutum daya ne cikin su ya tsere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: