Connect with us

Labarai

Ganduje ya naɗa Ƙofar na’isa babban mataimakinsa kan kafafen yaɗa labarai

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da naɗa Abubakar Balarabe Ƙofar Naisa a matsayin babban mataimakinsa kan kafafen yaɗa labarai.

Kafin naɗashi a matsayin mataimaki na musamman, Ƙofar naisa shi ne wakilin gidan radio Kano a fadar gwamnatin kano.

Cikin takardar da aka aike a gareshi wanda aka bayyana Abubakar Ƙofar Naisa a matsayin jajirtacce kuma haziƙi wanda gwamnan ya ce cikin jajircewarsa zai taimaka wajen samun nasarar gwamnatin.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sake Ganawa Da ‘Yan Kwadago Akan Mafi Karancin Albashin Ma’aikata

Published

on

Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na sake gudanar da zama da ‘yan kungiyar kwadago ta NLC domin sake tattauna akan batun mafi karancin albashin ma’aikatan kasar.

Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan batun mafi karancin albashi ne ya aikewa da kungiyar ta kwadago wata wasika akan sake ganawa da su a ranar Talata mai zuwa.

Shugaban kwamitin Bukar Goni ne ya aikewa da kungiyar wasikar inda ya bukaci shugabannin kungiyoyin NLC da TUC su gayyaci ‘ya’yansu domin sake ganawa da su.

Kwamitin zai sake zama da kungiyar ta kwadago ne bayan kungiyar ta fice daga tattaunawar da su ka fara da kwamitin akan sabon mafi karancin albashi a ranar Larabar da ta gabata.

A ya yi tattaunawar da suka yi a makon da muke bankwana da ni kwamitin ya amince da sake yin gyaran a kan mafi karancin albashin na naira 48,000 inda bayan gbatarwa da kungiyar sabon albashin taki amincewa da shi.

Sai dai kungiyoyin kwadagon na neman gwamnatin tarayya ta amince da naira 615,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Kasar.

Continue Reading

Labarai

Ganduje Ya Bukaci Masu Hali Su Taimakawa Iyalan Wadanda Suka Mutu A Masallaci A Kano

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci masu hali da su taiimakawa iyalan wadanda suka mutu a harin masallaci da ya faru a garin Larabar Abasawa da ke Kano.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a birnin tarayya Abuja a yau Asabar.

Dr ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke mika sako ta’aziyyarsa ga wadanda lamarin ya rutsa da su.
Shugaban ya ce taimakawa mutanen zai taimaka matuka wajen rage musu radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya kuma nuna damuwarsa dangane da faruwar lamarin tare da mika sakon jaje ga wadanda lamarin ya rutsa dasu da kuma addu’ar Allah ya bai’wa wanda ke kwance a asibiti lafiya.

Ganduje na wannan rokon ne bayan wani matashi mai suna Shafi’u Abubakar mai shekaru 38 a duniya ya sanyawa wasu masallata wuta a lokacin da suke tsaka da sallar a Asuba a garin Larabar Abasawa da ke cikin karamar hukumar Gezawa ta Jihar Kano wanda hakan ya yi sanadaiyyar mutuwar mutane 15 ya yin da, wasu ke kwance a asibitin Murtala da ke Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin da matshin ya sanya wuta a cikin masallacin mutane 32 ne a ciki ke yin sallah ,inda ya sanya musu wuta sakamakon wani sabani na rabon gad

Continue Reading

Labarai

An Kama Jami’an Lafiya Da Suka Batar Da Mahaifa Da Cibiya Bayan Haihuwa A Kwara

Published

on

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kwara ta kama wasu jami’an lafiya biyar kan batar da mahaifa da cibiya bayan karbar haihuwar a wani asibiti a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Ejire Adeyemi ce ta tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a.

Kakakin ta ce lamarin ya faru ne a asibitin Iloffa da ke cikin karamar hukumar Oke-Ero a jihar a karshen makon da ya gabata.

Kakakin ta kara da cewa sun kama jami’an lafiyar ne bayan wanda ta haihu ta bukaci jami”an su gabatar mata da mahaifa da kuma cibiya bayan haihuwar jaririnnata, inda suka gaza gabatar mata wanda hakan ya sanya tashigar da kara ga jami’ansu.

Sai dai kakakin ya ce bayan tuhumar wadanda ake zargi sun bayyana cewa sun jefar da mahaifar amma suna tsammanin kare ya cinye ta.

Matar da ta shigar da karar ta bukaci da rundunar ‘yan sandan ta zurfafa bincike akan lamarin tare da yiwa jami’an hukunci akan abinda suka aikata.

 

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: