Mai magana da yawun ƴan sanda a Najeriya Frank Mba ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a Abuja.

Ya ce jami an sun rasa ransu yayin da suka nufi jihar Katsina.
Hatsarin ya faru a titin zaria zuwa Kaduna wanda yayi sanadiyyar jikkata wasu jami an da dama.

Tuni aka garzaya da waɗanda suka samu rauni zuwa asibiti don karɓar kulawa daga malaman lafiya.
