Kotun majistire mai lamba 18 da ke kan titin Zungeru a Kano ta yankewa wani Umar Abdurrahman hukuncin zaman gidan maza har shekaru biyu babu zaɓin tara bisa laifin lalata da ƙananan yara maza.

Matashin mai shekaru 30  ya amsa laifinsa bayan da aka karantawa mai shari a Muhammad Idris.

Tun da fari an kama matashin na lalata da wasu yara waɗanda sukace yana bsu naira 50  sannan yayi amfani da su.

Matashin ya girbi abinda ya shuka ne bayan da dubunsa ta cika aka miƙashi ga jami an tsaro wanda daga bisani suka gurfanar da shi a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: