DAGA RABIU SANUSI KATSINA.
Anyi kira ga al’ummar arewa da su tashi tsaye wajen gudanar da ayukan kungiyoyi dan tallafama al’umma da fidda su daga kangin talauci.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban gidauniyar Island Survive Foundation ta kasa watau Alh, Dr Bara’u Tanimu a yayin zantawa da wakilin mu na katsina, Rabi’u Sunusi
Shugaban yakuma bayyana yadda su ka ziyarci masarautun kananan hukumomin Mashi, Mani, da Dutsi .
Haka zalika shugaban ya kuma bayyana irin gudunmuwar da suka bada ga wa su kungiyoyi da na marayu da masarautun suka zakulo dan tallafa masu.
Dr Muhammad Bara’u Tanimu ya cigaba da cewa duk da kasancewar basu bude ofis a wadannan gurare ba, sun yi amfani da hakiman dan gano ma su bukatar a taimaka masu a halin da suka tsinci kan su na yau da kullum da maraici.
Sannan kuma ya bayyana sabon tsarin taimakon masu kananan sana’o’i da bashi da karamin bashi,amma bashin da babu ruwa a ciki.
Kuma yace bawai kawai ai ta daukar kaya ko kudi a ba mutane kyauta, a’a dan a kara farkar da su wajen daukar abin da mahimmanci yasa gidauniyar ta fiddo sabon tsarin ba ma su kananan sana’a bashi dan dan daukar lamarin da mahimman ci.
Dr, ya kuma yi kira ga al’umma da su kara kaimi wajen tallafama masu karamin karfi sakamakon kudu da sukayi nisa dan irin wannan shirye-shirye.
Daga karshe ya nuna godiya ga al’umma da suka ta tururuwa wajen karbar shirin su tare da bukatar hada karfi da gidauniyar island survive dan kawar da talauci, haka kuma shugaban ya yi kira da al’umma cewa gidauniyar island ta shirya da daukar nauyin yima masu cututukan Haniya da sauran wa su cututtuaka da za’ai ma aiki dan taimakon marasa karfi.