Dattijon mai shekaru fiye da 80 an yi garkuwa da shi ne tsawon kwana biyu da wuni ɗaya yana hannun mutanen.

“Tsawon kwana biyu da wuni ɗaya ko fitsari sai dai na yi a jikina” Inji wannan dattijon.
Bayan sun saceshi suka kaishi wani kango da ke unguwar mariri a Kano.

Dubun masu garkuwa da mutanen ta cika ne bayan sun yi garkuwa da wannan dattijo tare da yiwa wani mutum fashi wanda suka kwace motarsa da kudade.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta faɗaɗa aikinta na tsamo masu laifin wamda ta bi wasu har jihohin jigawa da kaduna.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu A. Sani ne yayi holen masu aikata laifuka ciki har da ƴan fashi da makami da masu garkuwa daa mutane.
Cikin kayayyakin da rundunar ta yi nasarar kuɓutarwa akwai motoci da babura har ma da babur mai ƙafa uku.
Sannan rundunar ta yi nasarar kwato muggan makamai tare da kayan maye masu kimar kuɗi na miliyoyin naira.
Kwamishinan yayi kira ga al ummar Kano da su cigaba da bawa rundunar haɗin kai ta hanyar bin doka da oda tare da sa ido a unguwanni don daƙile muggan laifuka.