Akalla Mutane 3 ne suka mutu a hadarin jirgi mai saukar ungulu da yayi a Legas

A yanzu haka dai Kwararrun Jami’an sashin hadurran jirgin sama a Najeriya, suna kaddamar da bincike don gano musababbin hadarin jirgi mai saukar Ungulun da ya rikito kan gidaje a unguwar Opebi dake karamar hukumar Ikeja dake Legas a jiya Juma’a.
Da yake karin haske kan hadarin, babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa a jihar ta Legas , Dakta Femi Osanyintolu, yace mutane biyu sun rasa rayukansu, sai dai daga bisani rahotanni sun ce cikon na ukunsu shi ma wanda a baya ke halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Rahotanni sun ce fasinjan da ba’a bayyana ko waye shi ba, ya mutu ne a asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Legas dake Ikeja.
Majiyar mu ta Rfi hausa ta rawaito cewa Bayanai sun ce jirgi mai saukar ungulun da yayi hadari mai suna Bell 206, mallakin kamfanin Quorum Aviation, ya tashi zuwa Legas ne daga birnin Fatakwal, dauke da matuka biyu da fasinja daya.
