Ƙungiyar yan jaridu rehen jihar Kaduna ta umarci mambobinta kan marawa ƙungiyar kwadago ta ƙasa a Najeriya NLC don gudanar da zanga zangar lumana a gobe Litinin.

A cikin sanarwar da sakataren ƙungiyar kwamaret Femi John Adi ya fitar, ƙungiyar ƴan jaridu a Kaduna sun mambobinta da su marawa ƙungiyar kwadago baya a kan zanga zangar da za agudanar a gobe.

Ƙungiyar kwadago ta sha alwashin tsunduma yajin aiki tare da zanga zanga daga gobe litinin sakamakon ƙarin farashin man fetur da wutar lantarki wanda gwamnatin ƙasar ta yi.

Ana sa ran dukkan ma aikatan gwamnati da masu zaman kansu a Najeriya za su marawa ƙungiyar kwadago baya a kan ƙudirinta na ganin an janye ƙarin farashin kuɗin.

A makon da muka yi bankwana da shi wata kotu ta yi umarnin hani ga ƙungiyar kwadago kan zanga zanga da yajin aikin da za ta yi, wanda ƙungiyar ta bijirewa umarnin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: