Cibiyar dakile yaduwar cutuka a Najeriya NCDC ta bayyana cewar mutane 4308 ne suka rage masu cutar mashakon numfashi ta Korona.

Adadin mutanen ya karu ne bayan an samu Karin mutane 113 masu dauke da cutar a jiya Talata.

Wannan ke nuni da cewar Jimillar mutanen da suka taba kamuwa da cutar a najeriya dai ya kai 62, 224, sai mutane 57,916 da suka warke sannan mutane 1,135 da cutar ta yi ajali.

Tuni ƙasar ta fara komawa ayyukanta wanda ko a baya bayannan sai da aka bawa dalibai damar cigaba da daukar darasu bayan an rufe makarantun tsawon lokaci.

An samu saukin masu kamuwa da cutar a faɗin kasashe daban daban kuma mafi yawa daga ciki sun fara komawa ayyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: