Akalla masallatai 2 aka ƙona tare da ƙona shagunan musulmi a garin Nsukka a jihar Enugu.

Musulmi da dama sun tsere don gudun afka musu a jihar.

Shugaban ƙungiyar Musulmi a Nsukka Alhaji SanI YA BAYYANAWA bbc Hausa cewar an lalata babban masallacin juma a na garin tare da wani masalaci duka a Nsukka.

Muhammad Adam Yusuf guda ne cikin mutanen da BBC suka tattauna da shi, y ace an kona shagunan musulmi tare da raunata da yawa daga ciki, yayinda wasu tuni suka koma jihohinsu.

Lamarin dai ya samo asali ne sakamkon sabani da aka samu da wata mata musulma da wani mai hayar babur lamarin da ya sa mutanen garin suka afkawa musulmi tareda kona dukiyoyinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: