Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewar gwamnatinsa ta kashe biliyan ɗaya da miliyan ɗari takwas 1.8 kuɗin makarantar ɗalibai da ke karatu a jami’o’i nagida da na waje.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar zartarwa na jihar bayan ɗaliban da suka kammala karatu a jami’ar American University da ke Yola.

Ɗalibai 20 da suka yi kwazo tate da gabatar da shaidar kammala karatun ga gwamna Ganduje, an yi musu alƙawarin sama musu gurbin aiki matuƙar an buƙaci hakan a nan gaba.

Cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar, ya ce gwamnatin Ganduje na ɗaukar nauyin ɗalibai 1150 da ya gada daga gwamnatin Kwankwaso.

Ganduje ya yabawa ɗaliban a bisa ƙoƙarin da suka yi na samun kyakkyawan sakamakon karatunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: