Hukumar kashe gobara a jihar Kaduna ta ce an samu rahoton tashin gobara har sau 615 kuma mutane 76 ne suka mutu a shekarar 2020 da ta gabata.

Shugaban hukumar Paul Aboi ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsu kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Kaduna.
Ya ce mutane 139 ne suska jikkata a sanadin gobara a shekarar da ta gabata.

Sannan an rasa dukiya ta naira biliyan biyu da rabi kuma an ceto dukiyar naira biliyan biyar.

A cewar shugaban hukumar, an samu ƙaruwar tashin gobara a shekarar 2020 la’akari shekarar 2019 gobarar ta faru sau 523.
Ya ce akowanne lokaci suna buƙatar sanar da su cikin gaggawa a yayin da aka samu tashin gobarar.