Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jinjinawa shugaba Buhari bisa nada Auwal Zubair a matsayin hafsan sojin ruwa a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwarya fitar ya ce Auwal Zubair ɗan jihar Kano ne da ya fito daga yankin ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano.
Gwamna Ganduje ya ce an ajiye kwarya a gurbinta ganin yadda hafsan sojin ruwan Auwal Zubair ya jajirce a kan aikinsa tare da samun kwarew a fanni daban daban.

Ganduje ya yabawa shugaban ƙasa Buhari a bisa naɗa sabbin hafsin sojin Najeriya wanda ya ce dukkanin waɗanda aka ɗora sun cancanta da matsayin da suke kai.

Gwamna Ganduje ya buƙaci sabbin hafsin sojin Najeriya da su saka kwarwwar aiki wajen fuskantar matsalar tsaro da Najeriya ke ciki a halin yanzu.
Daga jihar Borno ma gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nuna farin cikinsa dangane da sauke manyan hafsoshin tsaro a Najeriya.
A jiya Talata shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin naɗa sabbin hafsoshin tsaro bayan ya yiwa tsofaffin ritaya.
An naɗa Janar Leo Irabo a matsayin babban hafsan tsaron Najeriya
Sai Janar I. Attahiru babban hafsan sojin ƙasa
Sannan Rear Admiral A.Z Gambo babban hafsan sojin ruwa
Sannan Air Vice-marsahal I.O Amao a matsayin babban hafsan sojin sama.
Tun tuni ake ta kiraye kiraye ga shugaban da ya sauke hafsoshin tsaron Najeriya ganin yadda al’amarin tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa.
Cikin mutanen da suke kiraye-kiraye a sauke manyan hafsoshin tsaron akwai gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum
Gwamna Zulum ya bayyana jin dadinsa cikin wata sanarwa da mai Magana da yawunsa Isah Gusau ya fitar, wanda ya tabbatar da cewar zai bayar da hadin kai ga sabbin hafsoshin tsaron da aka nada.