Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da yin muƙabala tsakanin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara da malaman Kano.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Mallam Abba Anwar ya fitar. Gwamnan ya ce za a gayyato mutane da za su yi alƙalanci a yayin gudanar da muƙabalar.
Malamai daga ɗariƙa daban-daban ne za su yi muƙabalar a kan iƙirarin da Sheik Abduljabbar ke yi.

Gwamnan ya ce nan da kwanaki ƙalilan za agudanar da muƙabalar.

Zaman zai samu halartar ɓangare daban-daban na gwamnati tun daga kwamishinan harkokin shari’a na jihar Kano da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano da sauran su.
Za a saka muƙabalar kai tsaye a kafafen yaɗa labarai sannan gwamnan ya buƙaci al’ummar Kano da su zauna lafiya kafin da yayin da kuma bayan kammala muƙabalar.