A yau 16 ga watan Fabrairu babbar kotun majistire mai lamba takwas ta saka don ci gaba da sauraron ƙarar matar nan da ake zargi ta kashe ƴar aikin ta.

Ana zargin Fatima Hamza da kashe yar aikin ta a Kano ta hanyar azabtarwa, baya ga rashin kulawa da lafiyarta bayan da ake zargi wani muzuru ya cijeta kamar yadda hukumar yan sanda ta bayyana.
An gurfanar da Fatima Hamza a gaban kotun majistire mai lamba takwas da ke unguwar gyaɗi-gyaɗi a Kano.

Sai dai hukumar gidan gyaran hali ta bayyana cewar wadda ake zargi na cikin tsananin rashin lafiya, wanda ya sa ba su samu damar halartar kotun ba.

Ko da a makon da ya gabata sai da aka bayyana dalilai na buƙatar bayar da belin wadda ake zargi, kuma a cikin dalilan akwai rashin lafiyar da take ciki kamar yadda lauyan da ya jagoranci lauyoyin wadda ake zargi Ibrahim Cheɗi ya bayyana.
Kotun ta sake saka ranar 23 ga watan da muke ciki don duba yuwuwar bayar da belin wadda ake zargi.