Rundunar sojin sama a Najeriya ta ce za ta sanar da cikakken bayani a bisa tarwatsewar jirginta wanda ya faru a makon jiya.

Babban hafsin sojin sama a Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ne ya sanar da hakan a sakamakon wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwar zamani wanda mayaƙan Boko Haram su ka ɗauki alhaki.
Mayaƙan Boko Haram ne su ka ɗauki alhakin baro jirgin a cikin wani faifan bidiyo wanda su ka nuna sashe daban-daban a cikin sa.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar sojin sama Edward Gabkwet ya ce za su ci gaba da aiki da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da tsare rayuka da lafiyar al’umma.

A ranar Larabar makon jiya ne jirgin sojin ya ɓata ɗauke da mutane biyu yayin da yake aikin murƙushe mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.
