Ministan Shari’a da shugaban jam iyyar APC na ƙasa Adam Oshiomhole sun ce INEC ta gaggauta wanke ‘yan takarar APC na Zamfara

Abin da kawai kotun ta yi, shi ne korar karar ta yi, bayan wanda ya kai karar yace ya janye kara, ba ya ja da Kotun Tarayya ta Abuja wadda a makon da ya gabata ta jaddada hukuncin Babbar Kotun Tarayya, ta ce ba a yi zaben ‘yan takarar APC a Zamfara ba.
Har yanzu dai babu ɗan takarar APC a zamfara, a dai dai lokacin da ake shirin fara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa nan da awanni 48 a Najeriya.

