Hukumar kare fararen hula a Najeriya reshen jihar Kwara, ta kama wasu mutane huɗu bisa zargin aikata fyaɗe kuma su ka kashe ta.

Mai Magana da yawun hukumar Babawale Zaid Afolabi ne ya bayyana wa ƴan jarida hakan a yayin gana wa da su.

Ya ce a ranar 2 ga watan Afrilun shekarar da muke ciki, su ka samu ƙorafi daga wani Alhaji Musa Waziri wanda ya bayyana musu ɓatan wata mai suna Aisha Sani.

Lamarin da ya sa jami’an su ka yi hadin gwiwa da yan sa kai da kuma ɓagaren ƴan sanda har su ka kama mutane huɗu waɗanda ake zargi sun aikata fyaɗen sannan su ka kashe ta.

An gano gawar Aisha a cikin daji wadda aka same ta na  yanke kan ta.

Tuni su ka miƙa ƙorafin da waɗanda ake zargi zuwa ɓangaren ƴan sanda a jihar kuma za domin zurfafa bincike, wanda da zarar sun kammala za a kai waɗanda ake zargi gaban kotu domin a yanke musu hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: