Hukumar zaɓe mai zaman kantaba Najeriya INEC ta saka ranar 18 ga watan Fabrairun shekarar 2023 a matsayin ranar da za a fara gudanar da babban zaɓen shugabanni a ƙasar.

Shugaban hukumar a Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan a yau Laraba.

Adadin kwanaki 660 kenan a nan gaba.

Hukumar ta ce za ta saki jadawalin zaɓen shekarar 2023 a watan Nuwamban shekarar da muke ciki.

Idan ba a manta ba, hukumar ta sanar da cewar za ta fara yin rijistar katin zaɓe na dindindin ga ƴan ƙasar a ƙarshen watan Yuli na shekarar da muke ciki.

Kuma za a yiwa waɗanda ba su da shi da kuma waɗanda shekarun su ya kai a wannan lokaci.

Sannan hukumar ta yi watsi da batun amfanin da katin lambar shaidar ɗan ƙasa a yayin yin rijistar katin zaɓen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: