Aƙalla mayaƙan Boko Haram goma aka kashe yayin wani hari da su ka kitsa kaiwa garin Rann da ke jihar Borno.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile harin mayaƙan Boko Haram tare da kashe wasu goma daga cikin su.

Baya ga mutanen da aka kashe an kwato wasu makamai daga hannun ƴan ƙungiyar Boko Haram kamar yadda rundunar sojin ta fitar da sanarwar hakan.

Daga cikin makaman da ka kwato akwai bindigu ƙirar AK47 masu yawa.

Hakan na zuwa ne awanni kaɗan bayan naɗa sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya.

Rundunar ta yi nasarar murƙushe harin yayin da su ka yi yunƙurin shiga garin Rann da ke ƙaramar hukumar Kala Balge ta jihar Borno sannan su ka kashe wasu daga cikin su.

Arewa maso gabashin Njaeriya na fama da rikicin Boko Haram sama da shekaru goma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: