Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci dukkan jami’an tsaron ƙasar da su yi aiki da kwarewa wajen ceto ɗaliban da aka sace a Neja.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a ckin wata sanarwa da mai Magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar.
Sanarwar ta umarci jami’an tsaro da su yi aiki cikin gaggawa tare da kwarewa wajen ceto ɗaliban da aka sace a makaranatar islamiyya ta Tegina a jihar.

A ƙarshen makon da ya gabata ƴan bindiga su ka shiga cikin garin tare da sace ɗaliban islamiyyar tare da malamansu ana zargin ma har da matan aure a ciki.

Shugaban makaranatar ya zanta da yan bindigan da su ka sace ɗaliban har ya buƙaci da kada su taɓa lafiyar ɗaliban da malaman su.
Sannan y ace har da ƴaƴan sa biyar a cikin waɗana aka sace a makaranatr.
Zuwa yanzu dai ya ce sun samu rahoton ɗalibai 136 waɗanda iyayensu su ka tabbatar da cewar bas u ga ƴaƴan su ba.
Ana zargin dalibai da malaman islamiyyar da yan bindiga su ka sace sun haura 200, yayin da adadin ɗaliban da ke karatu su ka kai 302.
Ƴan bindigan sun firgita mutanen garin da harbin bindiga yayin da su ka shiga makarantar da nufin sace ɗaliban.
Ko da yake an saki wasu ɗalibai da aka ce ƙanana ne.