Daga Tijjani Adamu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ce a cikin kwanaki tara ta kama ‘yan Daba dari tara da 50 a fadin jihar nan.
Kwamishinan ‘yansandan jiha, CP Muhammad Wakili ne ya bayyana hakan yayin da ‘yan kwamatin samar da zaman lafiya a harkokin zabe na jihar Kano, suka kai masa ziyara jiya a ofishin sa.
CP Wakili, ya ce ‘yan daban da ake zargi sun kama sune a wurare daban-daban na cikin kwaryar birni tare da mugan makamai a tattare dasu.
Ya kuma ce a cikin mutane 950 an gurfanar da mutane 750 wadanda tini aka tura su gidajen Yari daban-daban a fadin jihar nan wadanda kuma suke jiran a kammala yanke masu hukunci a kotuna.
CP Wakili, ya kuma kara da cewar wadanda aka kama cikin su akwai masu dauke da mugan makamai sai kuma wasun su an kama su ne da miyagun kwayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: