Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana cewar tubabbun mayaƙan Boo Haram na saka jihar cikin zulumi.

Gwamna Zulum yay i bayanin yadda mayaƙan ke tuba wanda ya ce tuban su abu ne mai matuƙar wahala mutane sun karɓe su hannu biyu don ci gaba a rayuwa da su.
Haka zalika a ɓangaren jami’an tsaro ma za su shiga damuwa ganin yadda mayakan ke tuba duk da kashe abokan aikin su da su ka yi.
babagana Zulum ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ziyarci sojoji da shugabannin yankuna a Bama da Gwoza.

Ya ce al’ummar jihar na tsaka mai wuya ganin yadda ake samun tubabbun Boko Haram waɗanda ba lallai ne mutane su aminta da su don ci gaba da rayuwa da sub a.

Gwamnan ya ce har yanzu mutane bas u daina jin radadin zafin kashe-kashen da mayakan Boko Haram su ka yi wa ƴan uwan su ba.
Sannan ya ce abu ne mawuyaci mutane su gamsu da tuban su bayan sun rasa makusantan su a dalilin Boko Haram.
Jihar Borno na shan fama da rikicin mayaƙan Boko Haram sama da shekaru goma.