Asibitin duba masu larurar ƙwaƙalwa ya tabbatar da cewar Abduljabbar Kabara ba shi da matsalar ƙwaƙwalwa.

Alƙalin kotun ya tuntuɓi rahoton gwajinmatsalar kunne da aka aike a yi wa malamin a asibitin Murtala kuma shi ma an ce ba shi da matsalar kunne.
Alƙalin Kotun shari’ar musulunci da ke ƙofar kudu a Kano Ibrahim Sarki Yola ne ya bayar da umarnin duba ƙwaƙwalwar malamin bayan an karanta masa dukkanin tuhumar da ake masa amma ya gaza cewa komai.

Lauyoyin Abduljabbar ba su iya zuwa kotun ba a yau sai guda ɗaya daga cikin su Barista Haruna magashi kuma ya ce ya janye daga kare malamin.

Lauyan ya ce dalilin rashin zuwan sauran lauyoyin ma bai wuce janye wa daga kare malamin ba.
Gwamnatin Kano ce ta gurfanar da malamin a gaban kotu bayan anzarge shi da ɓatanci ga annabi S.A.W da kuma kalaman tinziri.