Gwamnan jihar Kaduna ya ce zai toshe layukan sadarwar wayar salula a jihar.

Sai dai gwamnan ya ce ba dukkanin kananan hukumomin za a rufe ba.
Gwamna El’rufai ya ce ko a yau al’umar jihar su ka amince za a rufe layukan wayar a jihar za a rufe a yau Laraba.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ake fama da rikicin yan bindiga wanda hakan ya haifar da asarar rayuka mai yawa.

A na zargin za a toshe layukan ne a kanan hukumomin da abin ya fi ta’azzara.