Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da kashe ƴan bindiga 32 wadanda su ke koƙarin tsere wa daga dajin Zamfara zuwa Neja.

Wata majiya ta tabbatar da cewar ƴan bindigan na tserewa ne a sakamakon luguden wuta da dakarun soji ke yi musu a dazukan Zamfara.

Sai dai daga cikin jami’an gtsaron an kashe ƴan sanda biyar yayin da su ke musayar wuta da yan bindigan.

Al’amarin ya faru ne a Bangu Gari da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Ƴan bindigan na tsere wa daga dazukan Tsafe tare da  makamai masu hatsari.

An ɗauki ɗamarar yaƙi da ƴan bindiga a Zamafara tun bayan rufe hanyoyin sadarwar wayar salula a jihar.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da ake fuskantar rikicin ƴan bindiga wanda hakan ya sa aka rasa rayuka da dukiya  mai yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: