A yau a ka gudanar da zaɓen shuwagaban jam’iyyar APC a matakin jihar Kano.

Sai dai jam’iyyar ta kasu gida biyu yayin da wasu su ka juyawa tsagen gwamnatin jihar baya.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya jagoranci zaɓen shugaban jam’iyyar wanda ya gudana a filin wasa na Sani bacha da ke unguwar ƙofar mata.

Yayin da ƴaƴan jam’iyyar tsagen tsohon gwamnan Kano kuma sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau su ka gudanar da nasu zaben a bakin Sani Abacha Youth Center.

Ƴan sanda sun rufe wajen da tsagen Shekarau za su yi zaɓen sai dai sun bayyana cewar sun gudanar da zaɓen su kuma Alhaji Haruna Zago ne ya lashe zaɓen kujerar shugaban jam’iyyar APC a Kano.

Kafin zaɓen shugaban jam’iyyar, wasu daga cikin santocin Kano da ƴan majalisar tarayya sun yi ƙarar gwamnatin Kano a kan rashin basu haƙƙin gudanar da demokaraɗiyya a cikin jam’iyyar.

A halin yanzu dai an zuba ido don duba ɓangaren da uwar jam’iyyar ta ƙaa za ta karɓi sakamakonsu wanda hakan zai tabbatar da shugaban jam’iyyar a jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: