Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun sanar da soke dokar bayar da tazara a masallacin Ka’aba da na Madina.

A wata sanarwa da hukumomi a masallatan su ka sanar sunce za a ɗage dokar ne gaba ɗaya daga ranar Lahadi.

Hakan na zuwa ne bayan da ma’aikatar harkokin cikin gida ta bayar da umarnin bude masallatan gaba ɗaya tare da sassauta dokar wanda aka saka don gudun yaduwar cutar Korona.

Sassauta dokar na nufin bayar da dama wajen gudanar da ibada ba tare da tazara ba, a yayin gudanar da sallah, safa da marwa da uma ɗawafi.

Amma hukumomin sun ce mutanen da aka yi wa allurar rigakafin cutar karo biyu ne kaɗai za su ci gajiyar ɗage dokar.

Hukumar saudiyya ta sanya dokokin bayar da tazara da sauran dokoki a ƙasar don hana yaduwar cutar Korona.

An fara sassauta dokar Korona a kasashe daban-daban bayan samun raguwar masu kamuwa da cutar, yayin da ƙasar Saudiyya ta ci ƙarfin cutar wajen yaƙi da ita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: