Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 4:30 na yamma yayin da ake tsaka da cin kasuwar Goronyo a jihar.

Ƴan bindigan sun zagaye kasuwar sannan su ka fara harbin mutane lamarin da ya sanya da yawa su ka rasa rayuwarsu

Aƙalla mutane 60 ake zargi ƴan bindiga sun hallaka a wata kasuwar da ke ci mako-mako a jihar Sokoto.

Al’amarin ya faru a ranar Lahadi yayin da ƴan kasuwa da masu siyayya ke tsaka da hada-hada a cikin kasuwar.

Ƴan bindiga sun shiga kasuwar Goronyo a ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto sannan su ka kashe ƴan kasuwar da masu siyayya a kasuwar.

Awanni da dama ƴan bindigan su ka shafe a cikin kasuwar kuma ake zargi sun kwashi kayan abinci bayan mutane sun gudu don tsira da rayuwarsu.

Baya ga mutanen da ƴan bindigan su ka kashe akwai wasu da dama wadanda ƴan bindiga su ka raunata.

Har zuwa lokacin da mu ke kammala wannan labara babu wata sanarwa a hukumance wadda ta tabbatar da kashe mutanen.

Mun yi ƙoƙarin ji daga bakin ƴan sandan jihar yayin da mu ka tuntuɓi kakakin ƴan sandan jihar amma ba mu sameshi ba a wayar tarho.

A na zargin mayaƙan Boko Haram na da sansani tare da karɓe wasu yankuna a jihar baya ga ƴan bindiga da su ka daɗe sun a ayyukan ta’addanci a ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: