Har yanzu ana ƙoƙari don ganin an ceto yaran mata guda biyu.

Hukumar kashe gobara a jihar Osun ta tabbatar da samun labarin wata mata da ta jefa ƴayanta mata biyu a cikin wata rijiya.

Matar ta efa ƴaƴan nata ne a cikin rijiya a yau da rana bayan fusata da ta yi kan matsin rayuwar da ta shiga a Najeriya.

Matar ta ce a baya matar na zaune a ƙasar waje daga baya kuma ta dawo Najeriya sannan wahalar da ta ke sha ce ta sanya ta aikata hakan..

Guda cikin maƙwaftan ya ce matar ta fara jefa babbar ƴar tata mai shekaru bakwai a cikin rijiyar sai kuma ta sake jefa ɗayar mai shekaru biyar a duniya.

Rahotanni sun tabbatar da cewar rijiyar da aka jefa yaran akwai ruwa mai yawa a cikin ta kuma ta kai nisan gaba 24.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara a jihar Ibrahim Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce a halin yanzu su na ƙoƙari don ganin sun ceto rayuwar yaran.

Leave a Reply

%d bloggers like this: