Rundunar ƴan sandan a Adamawa ta ce an hallaka mutane bakwai yayin da wasu da dama su ka jikkata a sabon hari da aka kai yankin Negga da ke ƙaramar hukumar Numan ta jihar.

Ƴan sandan sun yi zargin rikicin makiyaya da haifar da asarar rayukan a garin.

Jami’in hulda da jama’a na ƴan sandan a jihar DSP Yahaya Sulaiman ya ce mutane bakwai sun mutu sannan an jikkata wasu mutane bakwai a yayin rikicin.

Ya ƙara da cewa an kai wadanda su ka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyar su.

DSP Yahaya Sulaiman ya tabbatar da cewar an bai wa jami’an ƴan sanda na bangaren kula da manyan laifuka umarni domin ƙaddamar da bincke a kan lamarin.

Sannan za a zaƙulo wadanda ke da hannu a harin tare da ɗaukar mataki na doka a kan su.

Ƴan sanda a jihar sun buƙaci al’umma da u dinga ba su bayanai a kan duk wani al’amari da ke shirin faruwa domin kai ɗaukin gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: