Gwamnatin jihar Osun ta kama wani mai shekaru 43 da ya kashe ƴar cikin sa ta hanyar duka.

Kwamishiniyar mata da ƙananan yara da walwalar jama’a Olubukola Olaboopa ce ta sanar da haka a wata sanarwa.
Ta ce an kama mutumin mai suna Sanjo wand aya kashe ƴar cikin sa mai kimanin watanni biyu a duniya.

Ma’aikata a hukumarne su ka kama mutumin bayan sun sami bayanan sirri a kan abin da ya aikata.

Sai dai mutumin ya ce kukan yaron ne ya sa ta yi masa dukan da ya kai ga rasa rayuwar sa.
Sanjo ya ce matarsa ce ta tafi unguwa ta barshi da yarinyar ƴan watanni biyu a duniya kuma ya yi duk abin da zai yi don ganin yarinyar ta yi shiru daga kukan da ta ke amma ta ta yi shiru ba lamarin da ya sa ya daki yarinyar.
Mutumin ya ce bai daki yarinyar da niyyar ya kashe ta ba amma bayan yarinyar ta mutu ya binne ta a cikin gidan sa.
Tuni kwamishiniyar matan ta miƙa wanda ake zargi ga ƴan sanda a jihar domin fadaɗa bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu don a yi masa hukunci.
