Connect with us

Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Nan Da Makonni Uku

Published

on

Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki nan da makonni uku a nan gaba.

Ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wa’adin makonni uku don cika alƙawuran da ta ɗaukar musu ko kuma su tsunduma yajin aikin.

Hakan ya biyo bayan wani zaman majalisar ƙoli da ƙungiyar ta yi a Abuja.

Ƙungiyar ta ce ta yanke wannan hukunci ne duba ga rashin cika alƙawuran da gwamnatin ƙasar ta gaza cikawa tare da biyan su haƙƙoƙin su.

Shugaban da ya jagoranci zaman Farfesa Emmanuel Osodoke ya ce wannan ce mafita guda ɗaya da su ka cimma kuma ita ce hanyar da za su ɗauka.

Ƙungiyoyi da dama sun sha ɗaukar irin wannan mataki tare da nuna gazawar gwamnatin wajen rashin cika alƙawuran da ta ke ɗauka wanda hakan ke sa su tsunduma yajin aikin.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Jami’an Soji Sun Sami Nasarar Hallaka Yan Bindiga 216 Tare Da Kwato Makamai 3322

Published

on

Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa Jami’an soji sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga 216 tare da kwato makamai 332 a cikin makon da ya gabata.

Mai magana da yawun hedkwatar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu’a a birnin Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa jami’an sun kuma ceto mutane 161 da aka yi garkuwa da su a guurare daban-daban na kasar.

Buba ya ce daga cikin makaman da ‘yan bindigar suka kwato sun hada da bindiga kirar AK47 guda 131, bindigar PKT 3, bindigar M16 guda daya, bindiga kirar gida guda 43, bindigogin Danish 21 da sauransu.

Sannan Buba ya kara da cewa jami’an sun kwato harsasai kala daban-daban guda 5,994 da sauran makamai masu hadari.

Da ya ke karin haske akan ayyukan jami’an a yankin Neja Delta Janar Buba ya ce jami’an sun kwato litar danyan mai da aka sace 533,127 da kuma litar man dizal 24,520.

Kazalika ya kara da cewa an kuma kama mutane 24 masu satar man fetur a Kasar.

Buuba ya ce rundunar su ba za ta gajiya ba wajen kai hare-hare kan ‘yan ta’adda har zuwa lokacin da kasar za ta samu dawwamamman zaman lafiya.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Legas Ta Rufe Coci Biyar Da Guraren Shakatawa 19

Published

on

Gwamnatin Jihar Legas ta rufe wasu coci guda biyar da guraren shakatawa 19 a Jihar.

Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar Tokunbo Wahab ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kwamishinan ya ce gwamnatin Jihar ta dauki matakin ne sakamakon yawan damun mutane da kara da guraren ke yi.

Kwamishinan ya kara da cewa an rufe guuraren ne na wucin gadi har zuwa lokacin da za su bi dukkan dokokin muhalli a Jihar ba tare da saba ka’ida ba.

Kazalika Wahab ya ce hukumar ta kuma rufe wasu kasuwanni hudu da manyan kantuna sakamakon saba dokokin muhalli da suka yi.

Wahab ya ce ba za a bude dukkan guraren ba har sai kowannesu ya cika ka’idar hukumar.

Continue Reading

Labarai

Mutane Na Ci Gaba Da Fuskantar Tsananin Wahala Kafin Su Sami Man Fetur A Fadin Kasar

Published

on

A yayin da ake ci gaba da fuskantar layin dogo a gidajen man fetur a Kasar al’ummar kasar na ci gaba da kokawa akan yadda suke shafe tsawon wani lokaci akan layin neman man.

Mazauna kasar na ci gaba da kokawa akan matsalar karancin man fetur da tsadarsa a halin yanzu a wasu sassan Kasar.

A yayin da Matashiya TV ta zanta da wasu da ke kallayin neman man da kuma masu baburan adaidaita sahu sun bayyana yadda suke shan wahala kafin samun man tare da shafe tsawon wasu lukuuta kafin su samu.

Masu ababan hawan sun bayyana yadda gidajen man ke sayar da man amabanbanta farashi, inda suka bayyana cewa su na sayan man ne a sama da naira 900 a kowacce lita.

Sun kara da cewa wasu masu gidajen man na rufe gidajen mannasu ba tare da sayarwa ba bayan an kammala sauke musu daga tankokin Man.

Sannan sun yi kira ga hukumomi da su kawo karshen karancin man da ake fama dashi a Kasar.

Sai dai kamfanin mai na Kasa NNPC ya bayyana cewa ya gano matsalar da ta haddasa faruwar hakan a gidajen Man.

NNPC ya kara da cewa

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: