Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa na iya ƙoƙarinta don ganin an cika alƙawuran da aka ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake ƙaddamar da dogon titi a jihar Sokoto wanda minsitan shari’a ya wakilce shi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya buƙaci hakan yayin da yake ƙaddamar da wani dogon titi mai nisan kilomita 304 a jihar Sokoto.

Muhammadu Buhari wanda ministan shari’a a Najeriya Abubakar Malami ya wakilce shi, ya ce gwamnatin na mayar da hankalin don cika alkawuran da ta ɗauka a yayi da ta ke yaƙin neman zaɓe.

Ministan ya lissafo wasu manyan dokoki da mutane ke karyawa wanda ke haifar da haɗɗura da sauran abubuwan da su ka shafi rasa rayuka ko dukiya a kan hanya.
Daga cikin dokokin da ake karya wa akwai gudun wuce sa’a, ɗaukar kayan da su ka zarce ƙa’ida ajiye ababen hawa a gefen titin sabanin wurin da aka tanada don ajiye su da kuma zubar da fetur da dangogin man a kan tituna.
An ƙaddamar da titin da ya tashi daga Sokoto zuwa Tambuwal ya tafi har Kontagora sannan ya zarce Maƙera.
Ministan Malami ya ƙaddamar da titin ne a ranar Juma’a.