Gwamnatin jihar Sokoto ta haramta ayyukan ƴan sa kai a jihar baki ɗaya.

Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ne ya sanar da dakatar da ayyukan sa kai tare da ƙarfafa ayyukan ƴan banga.

Tambuwal ya faɗa a wani taro da a ka gudanar a jihar don tattauna matsalar tsaro, yace ayyukan ƴan sa kai su su ka sake damalmala rikicin yan bin diga a jihar zamafara.

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta haramta duk wani aikin yan sa kai tare da horon masu sha’awar taimaka wa tsaro a jihar da su shiga aikin banga.

Gwamnan ya ce duk wanda aka kama za a kai shi gidan yari tsawon shekaru 14 ko zabin tara naira 500,000.

Sannan suk wanda aka kama ɗauke da makami ba tare da ya na aikin banga ba to za a ɗaure shi shekaru bakwai a gidan yari ko biyan tara naira 200,000.

Wannan wani mataki ne da gwanatin ta sake ɗauka don ganin an kawo ƙarshen matsalar staro da ake fama da ita a jihar Sokoto.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: