Wata babbar kotu a Abuja ta rushe shugabancin jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin Abdullahi Abbas tare da bai wa Alhaji Haruna Ahmad Zago.

Kotun ta zartar da hukuncin ne a yau bayan da magoya bayan Ahmad Haruna Zago su ka kai ƙara a kan zaɓen da aka yi a kwanakin baya kadan.
Alkalin kotun Hamza Mu’azu ya karanto hukuncin ne yayin zaman kotun a yau Talata tare da ayyana shugabancin jam’iyyar APC tsagen Malam Ibrahim Shekarau a matsayin halastaccen shugabanci.

Tun bayan aiwatar da zaben shugabancin jam’iyyar a Kano rashin jituwa ya ƙara tsami a tsakanin bangaren biyu.

Yayin da aka yi zaɓen shugabannin jam’iyyar APC a Kano an yi kashi biyu tsagen gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da tsagen tsohon gwamna kuma sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau.
Jam’iyyar APC ta shiya kwamitin da zai bibiyi dukkanin matsalolin da ake fuskanta tare da ƙoƙorin yin sulhu a tsakanin su.