Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su yi ƙoƙarin kawo ƙarshen Boko Haram gabanin shekarar 2023.

Shugaban ya yi wannan kira ne ranar Juma’a a Abuja yayin da ya ke jan ragamar tattauna wa da masu ruwa da tsaki a kan tsaron Najeriya.
Ya ce lallai jami’an su kawo karshen mayaƙan Boko Haram kafin wa’adin mulkin sa na biyu ya cika.

Shugaba Buhari ya kai ziyarar aiki Maiduguri babban binrin jihar Borno a ranar Alhamis, kuma aranar sai da mayaƙan Boko Haram su ka harba makami mai linzami kusa da filin sauka da tashin jiragen sama.

Mutane da dama ne su ka rasa rayukansu a harin, yayin da wasu da dama su ka jikkata a sanadin harin.
Buhari ya sha alwashin kawo ƙarshen mayaƙan Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci kafin wa’adin mulkin sa na shekarar 2023 ya cika.
Kuma ya ce nan da wani lokaci dukkanin wani ta’addanci da ake fuskanta a Najeriya zai zama tarihi.