Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta musanta cewar shugaban ya kamu da annobar Korona.

Sanarwar ta fito ne bayan da aka samu wasu daga cikin hadiman shugaban sun kamu da cutar ciki har da mai magan da yawun sa malam Garba Shehu.

A wata tattauna wa da aka yi da Femi Adesina, ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai kamu da cutar Korona ba.

Sai dai bai bayyana sunyaen sauran mutanen da su ka kamu da cutar ba, saboda ba shi da ikon faɗa a cewar sa.

Ya ƙara da cewa abinda ya sani shi ne, duk wanda ya kamu da cutar Korona zai killace kan sa ne har sai ya warke, amma ahalin da ake ciki shugaban ya na kan ci gaba da ayyukan sa cikin koshin lafiya.

Malam Garba Shehu ne ya fara bayyana cewar ya kamu da cutar Korona duk da cewa ba ta yi tsanani ba a kan sa.

Wasu na zargin shugaba Buhari ya kamu da cutar, kasancewar an samu wasu daga cikin hadimansa na ɗauke da ita.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: