Ɗan takarar gwamnan Kano Abdussaalam Abdulkarin wamda aka fi sani da AA Zaura ya ce a shirye ya ke domin taimaka wa masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood domin ganin ta fita daga halin da ta tsinci kanta a ciki ta yadda za ta yi gogayya da sauran masana’antun shirya fina-finai na duniya.

AA Zaura ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi bayan kammala taron da kungiyar taurarin fina-finan Hausa ta Kannywood Celebrities Forum for AA Zaura ta shirya harma ta karrama shi.
Abdussalam Abdulkarim AA Zaura yace, zai yi duk mai yuwa domin kyautata sana’ar fina-finan Hausa tare da ɗora ta a gwadabe na zamani wanda dubban al’umma za su ci gaba da amfana.

Har ila yau ya ce, Masana’antar shirya fina-finan Hausa na da matuƙar muhimmanci a cikin al’umma, domin su na ba da gudunmawa wajen ci gaban al’umma ta fuskoki daban-daban, a don haka akwai buƙatar tallafa wa ɓangaren yadda ya kamata.

Masana’antar shirya fina-finan Kannywood dai ta ce a shirye ta ke ta haɗa kai da duk wanda ya shirya taimaka mata ta hanyar bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen shigarta da kuma kayayyakin aiki na zamani domin yin gogayya da takwarorinsu na ƙasashen duniya.

Shugaban kungiyar taurarin fina finan Hausa ta Kannywood Celebrities Forum TY Shaban ya shaida wa manema labarai cewa a halin yanzu masana’antar shirya fina-finan Hausa na cikin wani mawuyacin hali da ta ke buƙatar jajirtacce mutum wanda zai tallafeta ta hanyar ƙara horas da masu shirya fina-finai da masu ba da umarni da kuma su kansu masu fitowa a fina-finan da ilimin sana’ar ta yadda za ta ci gaba da tafiya daidai da al’adu.

“Duniyar shirya fina-finai ta ci gaba, sai dai a ɓangaren Kannywood akwai buƙatar fito da sabbin hanyoyi da dabaru domin bunƙasa sana’ar” inji TY Shaba.

Aminu Shareef Ahlan, na daga cikin wanda suka halarci taron, ya ce AA Zaura mutum ne mai nagarta wanda ya sha banban da sauran mutane idan a ka yi la’akari da yadda ya ke taimakon al’umma.

Jarumi a masana’antar Yakubu Muhammad ya ce masana’antar Kannywood na buƙatar samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ta hanyar gina manyan gidajen kallo na zamani wato ‘Cinemas’ tare da ƙara horas da ƴan Kannywood ilimin sana’ar shirya fina-finai a zamanance kuma ya na da yaƙinin cewa AA Zaura na da ƙwarin gwiwa da kishin tallafa musu.

Jaruman fina-finan Hausa da dama ne su ka halarci taron ganawar da kuma ba da lambar yabon, wanda suka hadar da Alhaji Kabiru Maikaba, Ibrahim Mandawari, Yakubu Muhammad, Ladidi Fagge, Kamal S Alkali, Salisu S. Fulani, Mansura Isah, Baballe Hayatu, Samira Ahmad, Aminu Shareef Ahlan, Tijjani Faraga da masu ba da umarni, da sauran masu ruwa da tsaki a kungiyar.

An yi taron a Kano ranar Asabar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: