Daga Amina Tahir Muhammad

Gwamnatin Kano ce dai ta yi ƙarar Abduljabbar Kabara a gaban kotu bisa zargin kalaman da za su iya tayar da fitina da kuma yin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Wata kotun shari’ar musulunci da ke Ƙofar Kudu ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Sarki Yola, ta umarci shaida na farko da ya gurfana a gabanta a ranar 17 ga Fabrairu, 2022 dangane da shari’ar Abduljabbar Nasiru Kabara.

Ana zargin Abduljabbar Kabara da yin saɓo da tunzura jama’a kamar yadda gwamnatin jihar Kano ta bayyana wa kotu.

Lauyan da ke kare Abduljabbar, ƙarƙashin jagorancin Ambali Obomeileh Muhammad SAN, ya buƙaci a dawo da shaida na farko da ya sake gurfana a gaban kotu domin yi masa tambayoyi.
Lauyan masu shigar da kara, karkashin jagorancin Barista Sa’ida Suraj SAN, ya ƙi amincewa da buƙatar, inda ya buƙaci kotun da ta janye bukatar.
“An ba su isasshen lokaci akalla makonni 4 don shiryawa a cewar lauyan gwamnati.
Sai dai alkali ya amince da buƙatar da su ka roƙa na sake gabatar da shaida na farko a gaban kotun.
An dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu da mu ke ciki.
Ana tuhumar Abduljabbar da tuhume-tuhume guda hudu da suka shafi zagi da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a lokacin karantarwarsa, wadanda suka saɓawa sashe na 382 (b) na dokar shari’ar musulunci ta jihar Kano da aka samar a shekarar 2000.